+2347067777762

Katsina State Nigeria

Get Update on our recent Gadgets & Tabs

Wednesday, 17 February 2021

Yadda zaka samu kudi da hotunan ka | Application mai biyan kudi Tsu

Assalama Alaikum warahamatullah wabarakatuhu 


Barkan ku da wannan lokacin dafan kowa yana lafiya. Allah ya kara rufa mana asiri duniya da lahira amin. 


Yadda zaka samu kudi da hutunan ka, da bidiyoyinka ta hanyar amfani da wannan Application din mai suna TSU ( Social That pays ).


Idan kai dan kasuwa ne ko kanada YouTube channel kodai wani social media da kakeso ka rinka samun kudi dashi to ya kamata ka tsaya ka karanta wannan rubutun gaba daya domin zai amfane ka, kuma zai sa ka suwancin ka ya zagaye duniya baki daya sannan kuma zasu rinka baka wani kaso daga cikin abubuwan da kake sawa a cikin manhajar su.


Kadan daga cikin abinda na samu kenam cikin kwana 3 ku kalli hoton nan na kasa


Kamar kullin a wannan Website namu muna nemo wasu applications ko wasu muhimmin abu wanda zai amfani mabiyan mu sannan muyi masu bayani dalla dalla akan yadda zasuyi amfani dashi domin cigan rayuwa da dai sauransu.  


A yau ma munzo maku da wani Application mai matuΖ™ar amfani sannan kuma bugu da kari har su yan kudade mutum zai samu idan yana amfani dashi ta yadda ya kamata. Kafin nayi maku baya nin wannan Application din mai amfani. 


Mutane da dama suna amfani da yanar gizo gizo wato Internet a koda yaushe amma zakaga kullin sune suke kashe kudin su basa samun ko sisi daga wannan yanar gizo gizo din misali. Kamar masu yin Instagram, Tiktok, likee, Snapchat, da dai sauran  su. Kunga duk wa'anan manyan shafi kan  sada zuminta ne  masu tarin mutane dayawa a cikin su sannan sunada cin data sosai.


Misali sai kaga mutum yanada mabiya a Instagram kima nin dubu 20 wani 30 wani ma har dubu 100,000 amma kuma baya samun ko sisi daga wannan mabiya dake gareshi. Abu daya ne ko biyu zai samu wasu suyi mashi like πŸ‘  wasu kuma suyi mashi comment to kunga wannan duk wata hanya ce wacce zakaita bata lokacin ka kuma kana bata kudin ka. 


Sannan kuma Tiktok kowa yasan wannan manhajar ta Tictok mafi aka sari video akeyi ko na dariya ko,na alja'abi,gasu nan dai dayawa shima mutum zaizo yayta hada video amma baya samun ko naira kuma wannan duk bata lokaci ne.


Shiyasa wannan website namu yaga ya kamata mu sanar da mutane akan wannan sabon Application din da akayi wanda komai nashi irin na Instagram ne, saidai su wannan suna bada wani kaso kadan daga cikin irin kudin da suke samu daga tallar da sauran kamfanoni suke sawa a cikin manhajar su. 


Ga sunan wannan Application din (TSU) Social thats pay.


Menene Tsu kuma ya ake amfani dashi har a samu kudi 


Da farko dai Tsu wani manhaja ne wanda mutum zai bode kamar yadda ake bude irin su Instagram kyauta to shima haka ake bude shi kyauta amma suna da dokoki wanda dole sai mutum ya cike wannan dokokin ko zai iya samun shiga wannan Application mai amfani.


Abubuwan da zakayi amfani dasu wajan rigista 


1.Gmail address 

2.Number waya 

3.ka zabi Password zaka hada nambobi da kalmomi misali kamar haka (@Password123456@) wannan misali ne. 

4.zaka sanya inviter name zaka sanya @hamza_kaita 


Ga link din Application din ka danna zai kaika playstore sai kayo download kayi rigista πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


https://invite.tsu.social/xYxv


Ku kalli wannan bidiyon domin sanin yadda ake amfani da wannan Application din 

https://youtu.be/MtqpL73lCIk

Ga hoto nan yadda ake rigista 

Wannan sune abinda suka fi so idan kayi rigista to sauran sai ka cike a ciki.


Ya ake amfani da Tsu har a samu kudi 


Da farko dai zaka rinka hada picture ko kuma video masu kyau kana yin posting kamar dai yadda kake yi a Instagram, to duk wanda yayi maka like, ko share, ko kuma yayi maka support na wannan abinda ka sanya to talla zata fito idan wannan tallar ta fito kuma wannan mutumin ya taba wannan tallar to zaa biya kamfanin Tsu kudi sukuma zasu baka 50% na kudin wannan tallar da aka taba ta dalilin hotonka ko bidiyonka 


Ga yadda zakayi posting hoto 


Ga yadda zakayi posting videos 

Hanya ta biyu wacce ake samun kudi da Tsu shine zaka iya gayyato abokanka yan uwanka dadai sauran duk wasu dake amfani da yanar gizo gizo sai ka basu link naka tare da numbobin gayyata domin su samu shiga suyi amfani da wannan Application to shima zaka samu kudi daga kamfani kyauta. 


Ga inda zakaga inviting name naka da link

Duk wanda kayi inviting yayi joining da link name naka zasu baka 0.25 dollars.. Amma dole sai yayi rigista ya sanya hoto a kalla ya sanya hoto koda guda daya ne sannan ya saita komai a cikin app din to da zaran duk yayi wannan abin za su baka ladan kawoshi da kayi kuma duk kyauta ne dan haka ya kamata ayi amfani da wannan damar.


Yadda zakayi ka rinka samun kudi


1.Zaka rinka like , ko kuma ka rinka taba talla a cikin hotuna kamar haka a yadda kake gani a wanan hoton na kasa2.Zaka rinka yiwa mutane support da share kamar ace idan abokin ka ya sanya hoto sai kayi support kuma kayi share nashi to shima Tsu zasu baka wani kaso daga cikin kudin da zasu samu idan aka taba talla dake akwai jikin wannan hoto dakayi supporting. Ga yadda akeyin support da kuma share ku kalli hoton nan na kasa.

Ya zan cire kudi na idan na tara daga Tsu 


Cire kudi abu ne mai sauki daga Tsu account amma a yansu hanya daya ce dole ne sai mutum ya bude asusun ajiya na PayPal, kyauta ake budeshi to idan ka bude duk lokacin daka tara kudin ka zaka iya tura su zuwa PayPal daga PayPal saika tura abinka zuwa bankin ka wato su zama naira. Amma fa ka sani sai kudin ka sunkai $15 dollars zaka iya cirewa Allah yasa mu dace amin.Ya zan bude PayPal account 

Ga wanda bashida PayPal account ga hanya mafi sauki zai shiga browser din shi sai ya danna www.paypal.com to da zaran kun sanya haka zakuga website nasu ya bude sai ku shiga rigista ko kuma create new account, ko ku shiga wannan zagayen da kuka anyi wato sign up ku cike duk abinda suke bukata shikenan.


Dokokin su na TSU


1.Basu yadda ka rinka daukar hutun wani ko video wani wanda shima yake sawa a manhajar su ka saka a naka ba idan suka gane ku kuma mai abin ya fada masu cewa ka dauki nashi to zasu kulle maka account. 


2.Basu yadda ka rinka sanya abinda ya shafi tsiraici ba shima zasu kulle maka account 


3.Basu yadda da comment ko posting na batan ci ga wani ba. 


Ku kalli wannan bidiyon domin sanin yadda ake amfani da wannan Application din 

πŸ‘‡πŸ‘‡
https://youtu.be/MtqpL73lCIk


A nan zan kawo karshen wannan darasi duk wanda yake da bukatar tambaya ko kuma wani abu da yake son karin bayani zai iya mana comment insha Allah zamu bashi amsa.


Mungode. 
No comments:
Write Comments

Facebook

Hey, to'get Our latest update .Subcribe here-
Join Our Newsletter